Da safiyar yau Alhamis ne aka gudanar da taron manema labarai game da taron tattaunawa karo na 12 na dandalin Xiangshan wanda za a gudanar a nan Beijing daga ran 17 zuwa 19 ga watan Satumban nan a cibiyar taro ta duniya ta Beijing, bisa taken “Hadin kai don kare tsarin duniya, da habaka ci gaban zaman lafiya”, inda za a gudanar da cikakken zama har sau 4 tare da kuma tarurruka 8 na rukuni-rukuni, da kuma taron shugabanni, da taron tattaunawa tsakanin matasan jami’an soja da masana, da na tattaunawa tsakanin manyan masana na Sin da na kasashen waje.
Wakilan da za su halarci taron sun hada da na kasashe masu arziki, da manyan kasashe masu tasowa, da kananan kasashe, da kuma wakilai daga yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula.
Ya zuwa yanzu, an shirya taron tsaf, kuma kasashe da shugabannin sassan tsaro, da hafsoshi, da kuma wakilai daga kungiyoyin kasa da kasa da na yankuna sama da 100 sun tabbatar za su halarci taron. Kana adadin wadanda suka yi rajista na wakilan taro, da masu sa ido, da ‘yan jarida ya kai wajen 1,800. (Amina Xu)