Al’ummar Egbe da ke karamar hukumar Yagba ta Yamma a jihar, a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu kan karuwar rashin tsaro da kuma kashe-kashen da aka yi a yankin.
Zanga-zangar ta biyo bayan wani mummunan tashin hankali da aka samu, inda mazauna yankin suka nuna fargaba da takaici kan abin da suka bayyana da tabarbarewar yanayin tsaro.
Egbe mai iyaka da jihar Kwara, an dade da saninta a matsayin daya daga cikin al’ummar Kogi ta Yamma da ke zaman lafiya da harkokin kasuwanci, amma al’amuran da suka faru a baya-bayan nan sun sa garin ya hautsine.
Zanga-zangar ta biyo bayan kashe jami’an ‘yansanda uku da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a wani shingen bincike a cikin garin Egbe.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kogi, SP William Ovye Aya, ya shaidawa manema labarai a Lokoja cewa, harin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba.
Ya kara da cewa kwamishinan ‘yansanda, Miller Dantawaye, nan take ya tura rundunar ‘yansanda zuwa yankin domin fatattakar maharan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp