Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya umurci sashin kula da tsarin samar da abinci na shugaban kasa (PFSCU) da ya gaggauta daukar mataki kan tsarin rarraba tallafin rancen kudi na naira biliyan 250 ga kananan manoma.
A kan haka, ya jaddada wa PFSCU da ta fito da taswirar aiwatar da yadda za a raba kudaden, yana mai cewa ya zama dole a kaucewa tsaiko da kuma tabbatar da cewa, shirin ya kai ga wadanda aka yi wa tanadi.
Sanata Shettima ya ba da umarnin ne a ranar Alhamis yayin taron kwamitin gudanarwa na PFSCU karo na 6, wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa a Abuja.
Shettima ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa baiwa PFSCU goyon bayan siyasa musamman, samar da takin zamani da kuma lamunin kudi da za a raba wa manoma a fadin Nijeriya.