Gwamnan Jihar kebbi, Dakta Nasir Idris (Kauran Gwandu) ya dakatar da Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya, Alhaji Yunusa Musa Ismail daga aiki.
Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafida ya sanya wa hannu aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi.
Takardar ta ce, “dakatarwar ta biyo bayan sakaci da aikin ma’aikatarsa, haka kuma Gwamnan ya umurci dakataccen Kwamishinan ya ba da dalilansa na kariya da zai hana a hukuntasa na sakaci da aikinsa a Matsayinsa na Kwamishinan”.
Dakatarwar da zo da mamaki ga mutane musamman a cikin Ma’aikatar lafiya ta Jihar, wanda takardar bata bayyana laifuffukan da ya aikata ba, sai dai ta nuna cewa an dakatar da shi ne saboda sakaci da aikinsa na harakokin kiwon lafiya a jihar.
Gwamnatin jihar ta sha alwashin bayyana sakacin aikin da Kwamishinan ya yi da zarar ta kammala bincike.
Don haka, an umurci babban jami’i a ma’aikatar da ya ci gaba da jan ragamar ayyukan ma’aikatar har zuwa lokacin da za a fitar da wata sabuwar sanarwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp