Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi, ya bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi; da takwaran sa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso da su Hakura da son ransu su dawo jam’iyyar PDP kamar yadda Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau yayi.
Makarfi, tsohon shugaban PDP, ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya bayyana a wani shiri na siyasa (Sunrise Daily) na gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
A cewar dan siyasar mai shekaru 66, jam’iyyu biyu ne kadai a Nijeriya – PDP da APC.
Ya kara da cewa, fusatattun matasa ne ke amfani da Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, a matsayin dan takararsu, inda ya kara da jan kunnen matasan da cewa, bai kamata su yanke shawarar zabar shugaban kasa ba cikin fushi. Obi dai ya bar PDP ne a watan Mayu inda kuma ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa Shekarau, wanda kuma tsohon gwamnan Kano ne, daga shekarar 2003 zuwa 2011, ya fice daga jam’iyyar NNPP bayan takun saka da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso.
Shugaban jam’iyyar, Iyorchia Ayu ya tarbi Shekarau a PDP ranar Litinin;