Shugaban Rundunar Sojin Sama (CAS), Air Marshal Hasan Bala Abubakar, ya yi kira kan ci gaba da yin haɗin gwiwa a tsakanin hukumomin tsaron Nijeriya, yana mai jaddada cewa; tsaron ƙasa aiki ne na haɗin gwiwa da ke buƙatar haɗin kai.
Air Marshal Abubakar, ya shaida wa shugabanni da wakilan ƴan ’uwan jami’an tsaro da suka halarci taron cewa; halartar tasu na da matuƙar muhimmanci, ”sanin kowa ne cewa; tsaron ƙasa aiki ne na kowa da kowa da ke buƙatar haɗin gwiwa.” Ya bayyana cewa, barazanar da ke kunno kai da suka haɗa da ta’addanci, satar mutane da sauran laifukan da suka shafi intanet, “abubuwa ne da suka ci garo da shari’a”, don haka; akwai buƙatar haɗin kan ɓangarorin tsaro daban-daban.
- Sojoji Sun Kama Ɗan Bindiga Ɗauke Da Makamai A Jihar Filato
- Jagororin Tsaro Da Na Sojoji Daga Sama Da Kasashe 100 Za Su Halarci Taro Na 12 Na Dandalin Xiangshan A Beijing
Da yake nuna irin muhimmiyar rawar da ɓangaren sojin sama ke takawa, ya bayyana su a matsayin masu bin dokoki da kula da horo fannin nasu, waɗanda kuma ayyukansu ke da matuƙar nuhimmanci tare da kuma da samun nasarori.
Tun da farko a jawabinsa na maraba, Shugaban Hukumar Air Vice Marshal (AVM) Idi Sani, ya jaddada muhimmancin rawar da shugaban yake takawa wajen tabbatar da ɗa’a, ladabtarwa, aiwatar da dokoki da kuma samar da ayyuka ga hukumar sojin saman.
A nasa jawabin Gwamnan Jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang, wanda sakataren gwamnatin jihar Architect Samuel Jatau, ya wakilce shi; ya yaba wa rundunar sojojin saman Nijeriya da sauran hukumomin tsaro a jihar, bisa namijin ƙoƙarin da suke yin a wanzar da zaman lafiya a faɗin jihar ta Filato.
A nasa jawabin, Air Marshal, AVM JA Usman, ya yaba wa hafsan hafsoshin sojin saman bisa jajircewarsa da kuma sadaukarwa wajen ciyar da harkokin sojin sama da sauran ma’aikata gaba. ya yi nuni da cewa, taron ya sabunta ƙudirin hukumar na yin amfani da fasahar zamani, ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙara ƙarfin gudanar da ayyuka yadda ya
kamata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp