A ranar 16 ga wata, mujallar Qiushi za ta wallafa sharhin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta mai taken “Zurfafa dunkulewar kasuwannin kasa ta bai daya”.
Cikin sharhinsa, shugaba Xi ya jaddada cewa, dunkulewar kasuwannin cikin kasar Sin, ita ce muhimmiyar shawarar da kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya yanke, kuma ba taimakawa kawai zai yi wajen kafa sabon tsarin neman ci gaba, da kuma biyan bukatun kasa na neman bunkasuwa mai inganci ba, har ma da biyan bukatun kasa na karfafa fasaharta cikin gasar dake tsakanin kasashen duniya. A matsayin kasa ta biyu dake da manyan kasuwannin yin sayayya a nan duniya, ya kamata kasar Sin ta dunkule manyan kasuwanni cikin kasa, ta yadda za ta tabbatar da karfinta na fuskantar kalubaloli iri-iri kamar yadda take fata.
Haka kuma, sharhin ya ce, ya kamata a mai da hankali kan manyan matsaloli, yayin da ake tsayawa tsayin daka wajen warware matsalolin baki daya daga tushe.
Xi ya kuma jaddada cewa, dunkulewar kasuwannin kasa wani aiki ne mai wahala, wanda kuma zai dauki dogon lokaci, shi ya sa, ya kamata a karfafa hadin gwiwar a tsakanin gwamnatin tsakiya da gwamnatocin matakai daban daban na kasar, da kuma tsakanin gwamnatocin wurare daban daban, ko a tsakanin gwamnati da kamfanoni, har ma a tsakanin kamfanoni daban daban, ta yadda za a cimma wannan buri da babban karfi. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp