Shugaba Bola Tinubu ya kammala hutun aikinsa kafin lokacin da aka tsara kuma zai koma Abuja a ranar Talata 16 ga Satumba, 2025, domin ci gaba da aikinsa.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, ya fitar a yammacin ranar Litinin, shugaban ya tafi kasar Faransa ne a ranar 4 ga watan Satumba, 2025, domin gudanar da wani ɓangare na hutunsa na shekara, kuma da farko an shirya yin hutun a tsakanin kasashen Faransa da Birtaniya.
A makon da ya gabata a birnin Paris, shugaba Tinubu ya yi wata liyafar cin abinci ta sirri da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, a fadar Elysée.
Shugabannin biyu sun yi nazari kan muhimman fannonin hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da Faransa, inda suka amince da zurfafa hadin gwiwa don samun ci gaban juna da kwanciyar hankali a duniya.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa ba a bayar da wani dalili na sauya wannan hutun ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp