Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin, a ranar Litinin ya tsallake rijiya da baya, bayan da ayarinsa suka yi mummunan hatsari a kan hanyar zuwa karamar hukumar Maigatari a jihar.
Kamar yadda jaridar ‘Newspoint Nigeria’ ta ruwaito, Shugaban Majalisar na kan hanyar zuwa Maigatari ne domin halartar wani gangamin siyasa da aka shirya a karkashin wani shiri mai taken “Dandalin tattaunawar Gwamnati da Jama’a” (Government and the People Engagement Forum) a lokacin da lamarin ya afku.
- Gini Ya Rushe A Jigawa, Mutum 1 Ya Rasu, 7 Sun Jikkata
- Majalisar Dattawa Ce Kawai Za Ta Iya Dawo Da Sanata Natasha – Magatakardar Majalisa
Wani wanda lamarin ya afku a gabanshi, ya bayyana cewa ayarin motocin na kan hanyar zuwa wurin taron ne sai daya daga cikin motocin da ke bayar da kariya ga shugaban, wata mota kirar Toyota Hilux ɗauke da jami’an ‘yansanda ta ƙwace, sannan ta yi ta hantsalawa.
“Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo.
Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp