Sabon Kwamandan Rundunar Tsaro ta farin kaya (NSCDC) na Jihar Kano, Bala Bodinga ya ba da umarnin gudanar da sintiri a koda yaushe (ba dare ba rana), na tsawon sa’o’i 24 kan muhimman kadarori da kayayyakin more rayuwa na kasa a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
Umurnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Ibrahim Abdullahi ya fitar, wanda aka rabawa manema labarai a ranar Talata.
- Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
- Majalisar Dattawa Ce Kawai Za Ta Iya Dawo Da Sanata Natasha – Magatakardar Majalisa
Ya ce, kwamandan ya bayar da umarnin ne a lokacin da ya karbi mukamin a matsayin sabon kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kano.
“Bayan karbar mukaminsa na sabon kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kano, kwamared Bala Bodinga ya umurci jami’ansa da su sadaukar da kansu ga muhimmin aiki na tabbatar da amincin muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa.
“Kwamandan jihar ya ba da umarnin cewa, ba dare ba rana, cikin sa’o’i 24, dole jami’an hukumar su rika yin sintiri da sanya ido domin dakile ayyukan barayi da masu aikata laifuka a lunguna da sako na jihar,” inji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp