Tawagogin Sin da Amurka sun yi tattaunawar keke-da-keke, mai ma’ana da zurfi bisa girmama juna da daidaito, dangane da batutuwan tattalin arziki da cinikayya dake ci musu tuwo a kwarya, ciki har da batun TikTok, a jiya Litinin, inda suka cimma matsayar daidaita matsalolin ta hanyar tuntuba da tattaunawa a tsakaninsu.
Da farko dai, muhimmanci da tasirin kyautatuwar alakar cinikayya da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka, ba su kadai da al’ummominsu zai yi wa amfani ba, zai kara bunkasa harkokin cinikayya a duniya da kara tabbaci ga dangantakar kasa da kasa, baya ga gudunmawar da zai bayar ga tattalin arzikin duniya.
- Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba
- Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi
Kasar Sin ta dade da bayyana matsayarta cewa, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare hakkoki da muradun kamfanoninta, kuma ba za ta taba cimma yarjejeniya bisa watsi da muradunta na ci gaba da tsaron kasa da ma cikakken ’yancinta ba.
Wannan tattaunawar ta kara tabbatar min da alkiblar da ta dace kasa da kasa su bi domin tabbatar da zaman lafiya da gudanar da harkoki cikin lumana.
A bayan bayan nan, an aiwatar da jerin tattaunawa tsakanin Sin da Amurka karkashin jagorancin shugabanninsu, inda aka samu kyawawan sakamakon da ya kyautata alakarsu ta tattalin arziki da cinikayya. Wannan ya nuna shawarar da a kullum Sin ke bayarwa cewa, tattaunawa ita ce mafita ga dukkan rikice-rikice, maimakon amfani da karfi.
Kasar Sin ta sha nanata cewa, babu mai samun nasara a yakin cinikayya ko haraji. Mun ga yadda aka samu hauhawar farashin kayayyaki da karuwar rashin aikin yi da faduwar darajar hannayen jari a Amurka, a lokacin da ta kaddamar da yakin haraji, wanda ya nuna cewa, maimakon cimma abun da take fata na samun fifiko, asara aka samu da lalacewar muradun kamfanoni da ’yan kasuwar kasar.
Kowace kasa tana da cikakken iko da ’yancin zabar manufofi da matakan da ya dace da ita. Da Sin ta tsaya kai da fata cewa ba za ta ba da kai a yakin haraji da Amurka ta tayar ba, hakan ya sa Amurka yin karatun ta nutsu, kuma ta tuntubi bangaren Sin domin tattaunawa.
Wadannan misalai sun nuna mana cewa, akwai hanyoyi masu sauki da inganci na samun maslaha, kuma shawarwarin da Sin take gabatarwa, su ne suka dace da yanayin duniya a yanzu. Ba dole sai kowa ya samu abun da yake so ba, amma hawa teburin sulhu da tuntubar juna tana taka muhimmiyar rawa wajen warware sabani, da lalubo inda kowane bangare zai iya saki, domin a samu mafitar da za ta karbu ga kowa. Kuma irin wannan din, shi ne burin sabuwar Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya da shugaban kasar Sin ya gabatar a baya bayan nan. Duniya ba ta bukatar mayar da hannu agogo baya ta hanyar tayar da rikice-rikice da danniya da nuna fin karfi, zamani ya sauya kuma dole salon tafiyar da harkoki ya sauya, domin dacewa da yanayin da ake ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp