A ranar Talata ne shugaba Bola Tinubu ya dawo gida Abuja bayan ya shafe makonni biyu yana hutun shekara a birnin Paris na kasar Faransa.
Shugaban wanda ya iso filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, ya samu tarba daga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio; Shugaban ma’aikata, Femi Gbajabiamila; da Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.
Tinubu ya bar Nijeriya zuwa kasar Faransa ranar 4 ga Satumba, 2025, domin gudanar da wani bangare na hutun sa na shekara.