Ma’aikatan hukumar tara haraji ta kasa (FIRS) sun shiga makoki sakamakon mutuwar manyan ma’aikata hudu a wata gobara da ta tashi a ginin ‘Afriland Towers’ da ke kan titin Broad, Legas a ranar Talata.
Mamatan suna aiki ne a ɗaya daga cikin ofisoshin FIRS guda biyu dake hawa na shida da na bakwai na ginin a lokacin da lamarin ya faru.
A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban FIRS shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Dare Adekanmbi ya fitar, ya ce, wadanda lamarin ya rutsa da su, sun hada da Misis Ekelikhostse George (Mataimakiyar Darakta), Mista David Sunday-Jatto (Mataimakiyar Darakta), Misis Nkem Onyemelukwe (Babbar Manaja), da Mista Peter Ifaranmaye (Manaja).