Gwamnatin tarayya ta dawo da karatun tarihin Nijeriya a makarantu, inda tace ya zama wajibi a cikin manhajar ilimi ta kasa.
Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, tare da Karamar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmad, wanda ya bayyana hakan, ya bayyana matukar godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu bisa jajircewarsa wajen kawo sauyi mai ban mamaki a karkashin shirin Renewed Hope Agenda.
Sun jaddada cewa, karatun Tarihi ba tarihin abubuwan da suka gabata ba ne kawai, muhimmin tushe ne don nuna wa ‘yan ƙasa kishin ƙasarsu.
Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za su koyi sabon darasin da aka samar na ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya hada tarihin Nijeriya da Ilimin zamantakewar Jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp