A baya bayan nan, tawagar likitocin kasar Sin ta 24 dake aikin agajin kiwon lafiya a janhuriyar Nijar, ta gudanar da tiyatar ALT irinta ta farko da aka yi nasarar gudanarwa a yankin yammacin Afirka.
An gudanar da tiyatar ne a babban asibitin gwaji na kasar ta Nijar. Kuma ana gudanar da tiyatar ALT ne ta hanyar yankar wasu sassan fata da tsokar cinyar mara lafiya, domin dasawa a wasu sassan jikinsa da suka lalace sakamakon wata matsala.
Ana kallon nasarar da aka samu ta aiwatar da wannan tiyata a Nijar, a matsayin nasarar da za ta cike gibin da ke akwai a fannin, a yankin yammacin Afirka. (Saminu Alhassan)