A yau Alhamis 18 ga watan nan na Satumba ne aka gudanar da bikin cika shekaru 94, da kaddamar da yakin kin mamayar dakarun Japan a birnin Shenyang na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin. An kunna jiniya, tare da buga karaurawa domin tunawa da barkewar yakin da aka fara a wancan lokacin.
Daruruwan mutane, ciki har da tsofaffin sojoji da ‘yan uwansu, sun hallara a babban dandalin harabar gidan tarihi na 9.18 dake birnin Shenyang, domin karrama wadanda suka fafata a yakin da Sinawa suka gwabza da maharan Japan.
Da karfe 9:18 na safiyar yau din, wakilai 14 daga sassa daban daban suka buga karaurara sau 14, wanda hakan ke alamta shekaru 14 da aka shafe ana gwagwarmayar yakar dakarun mamaya na kasar Japan.
A ranar 18 ga watan Satumban shekarar 1931, sojojin Japan suka tarwatsa wani sashi na layin dogo dake karkashin ikonsu, a kusa da birnin Shenyang, tare da zargin sojojin kasar Sin da aikata barna, domin su fake da hakan wajen kai hari barikin sojojin Sin dake kusa da birnin na Shenyang a daren ranar, da kuma hakan ne suka kaddamar da mamayar da suka kitsa cikin kasar Sin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp