Gwamnatin tarayya yanzu ta shirya tsaf wajen ɗaukar mataki akan makarantun Sakandaren da basu da ƙwararrun Malamai a faɗin tarayya Nijeriya waɗanda basu da shaidar mallakar satifiket na cancantar damar koyarwa daga hukumar kula da lamurran Malaman makaranta ta ƙasa. Irin waɗannan makarantun da suk ɗauki irin Malaman da basu da satifiket na cancantar koyarwar daga hukumar daga yanzu za su rasa damar da ake basu ta zama cibiyar rubuta jarabawar (WAEC), (NECO),da sauran nau’oin jarabawa.
Gwamnatin tarayya tace irin irin waɗancan makarantun ba za’a amince masu su ci gaba da zama cibiyar rubuta jarabawa ba.
Wata takardar da aka turawa babban Rajistara na Hukumar kula da harkokin Malamai ta ƙasa, TRCN, daga ofishin Minisatan ilimi Dakta.Tunji Alausa “ Ma’aikatar ilimi ta bada umarnin cewar kamar yadda tsarin ilimin yake, wanda ake buƙatar, a samu bunƙasar ƙwarewa a aikin koyarwa na Malaman makaranta, daga yanzu duk wani lamarin daya shafi amincewa da cancantar zama cibiyar rubuta nau’oin jarabawa na Makarantun Sakandaren gwamnati da kuma na masu zaman kan su, wato WASSCE, NABTEB, NECO, da kuma NBIAS, abin zai zama ƙarshin ikon hukumar kula da harkokin, Malaman makaranta ta ƙasa, ita zata yi wa makarantun cancancewa ta ko sun cancanta da zama cibiyar rubuta jarabawa.”
- Gwamna Yusuf Ya Nuna Jin Daɗinsa Kan Yadda Kano Ta Zarce Legas, Oyo A Sakamakon NECO Na 2025
- Gwamnatin Tarayya Ba Ta Soke Jarabawar WAEC Da NECO Ba
Umarnin ya ci gaba da bayanin “,daga watan Maris 2027 WASSCE, Mayu 2027 NABTEB, Yuni 2027 NECO da Yuni 2027 SAISSCE, duk makarantar da ta kasance Malamanta ba suyi rajista ba,kuma basu lasin na koyarwa daga hukumar za a cire sunan makarantar daga kasancewa jibiyar rubuta jarabawa.”
Domin a samu hanya mafi sauƙi ta cimma burin muradin, “Malaman makaranta waɗanda basu yi karatun digiri na ilimi ba wato education a matsayin darasi a Jami’a, amma kuma sun samu ƙwarewa kan koyarwa a aji, da abin ya kai tsawon watanni goma sha biyu, an aba irin Malaman ƙwarin gwiwa na su yi rajista da hukumar kula da ilimin Malaman makaranta, kamar yadda sanarwar ta ƙara jaddadawa.
Tsarin ya ƙunshi na “ kwas na ƙwarewa kan lamarin koyarwa na gajeren lokaci wanda akan yi wata uku zuwa shida ne, bayan haka ne waɗanda suka yi kwas ɗin ne za su cancanci yin rajista da hukumar , har su samu Lasin na amincewa da sun cancanta su yi aikin koyarwa.”
Tsarin na ma’aikatar ilimin ya ƙara jan kunne na da akwai buƙatar tabbatar da cewaana amfani da shi tsarin dokar kamar yadda aka bayyna “a kuma samu dama ta wayar da kan duk masu ruwa da tsaki kan lamarin” a duk illahirin faɗin tarayyar Nijeriya”saboda kar abin ya kawo cikas na jarabawar da ta shafi ƴ aƴ an al’umma.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp