Ko shakka babu, tsarin tantance lafiya kafin a kai ga yin aure, yana da matuƙar amfani a tsanin al’umma.
Ya kamata a lura da cewa, idan aka gano guda daga cikin masu shirin yin aure yana ɗauke da wannan cuta, ba fa auren ake fasa yi ba, illa kawai dai za a ɗora shi a kan magani ne na tsawon wani lokaci, sannan kuma da zarar ya warke daga wannan ciwo na hanta, sai a ɗaura auren.
Daga cikin dalilan saukar da shari’a, akwai batun kiyaye lafiya. Saboda da haka, wannan tsari na tantance lafiya kafin aure; ya kamata ya zama wajibi a kan kowa da kowa.
dan guda daga cikin ma’aurata yana ɗauke da wannan cuta ta hanta, zai iya harbin aboki ko abokiyar zaman tasa; ba tare da ya sani ba, wannan shi ita ce babbar hikimar yin gwaje-gwaje a tsakanin masu shirin yin aure, kafin su kai ga yi.
- Nijeriya Na Asarar Kusan Naira Tiriliyan 17.9 Duk Shekara Sakamakon Cutar Hanta — Gwamnati
- Yadda Ake Hada Miyar Hanta
Don haka, hanyoyin da ciwon hanta ke yaɗuwa sun haɗa da:
1- Musayar yawu ta hanyar sumbatar juna- Ma’ana, ta hanyar sumbatar juna a tsakanin ma’aurata, idan guda daga cikinsu na ɗauke da cutar, nan da nan ɗayan shi ma zai kamu da cutar.
2- Gaurayewar jini ko haɗuwar jini- Haɗuwar jini, misali; idan wani ya yi amfani da reza ya yanke, ɗayan ya yi amfani da ita, zai iya kamuwa da cutar, ko kuma wani abu maikama da haka.
3- Ɓangaren saduwa a tsakanin ma’aurata- A wajen saduwa tsakanin mata da miji, ta hanyar haɗuwa maniyyi ko maziyyi da sauran makamantansu, wannan cuta za ta samu hanyar shigewa nan take da ɗaya daga cikinsu na ɗauke da ita.
Don haka, waɗannan hanyoyi da aka ambata dukkanninsu na iya faruwa a zamantakewar aure, kamar yadda masana kiwon lafiya suka sanar.
Saboda haka, ya zama wajibi mutane su kiyaye tare da bin ƙa’idojin waɗannan masana, musamman ta fuskar aiwatar da gwaje-gwaje, kafin a kai ga yin aure.
Wajibi ne ka kiyaye tare da kula da lafiyarka da kuma ta iyalinka, domin kuma sai an tambaye ka a kan yadda ka kula da ita. Sannan, yin wannan gwaji ba wani kayan gabas ba ne, duk da cewa; wasu na nuna tsoronsu a fili wajen zuwa a gwada su, wai a cewarsu; suna zaman-zamansu ka da ce; ba su da lafiya.
A nan, irin abin da Bahaushe yake cewa ne, “An gudu, ba a tsira ba”. Don haka, tun wuri kafin ku kai ga yin aure, ku je kai da yarinyar da za ka aura a gwada ku, a tabbatar da kwa ɗauke da wannan cuta ta hanta.
Haka nan kuma, su ma sauran ma’aurata; da zarar guda daga cikinsu, ya ji alamu ko an tabbatar masa da yana ɗauke da wannan cuta, ya yi ƙoƙarin taimaka wa abokin zaman nasa, ta hanyar zuwa yin gwaje-gwaje da kuma yin rigakafin kamuwa da cutar.
Mutane da dama, ba su san cewa; ana yin rigakafin wannan cuta ba, wanda abu ne da aka jima ana yi; ba lallai sai wanda ya kamu da cutar ba, kowa ma zai iya zuwa a yi masa kamar yadda masu iya magana ke cewa; “Rigakafi ya fi maganai”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp