Rundunar ƴansanda a Jihar Bauchi ta tabbatar da kama wata mata, wadda ake zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara bakwai mummunan rauni ta hanyar ƙona mata al’aura da wuka mai zafi a garin Magama Gumau, ƙaramar hukumar Toro.
Rahotanni sun ce matar ta zargi yarinyar da maita, lamarin da ya sa ta yi amfani da wuka da aka zafafata a wuta wajen ƙona jikinta. Ihun yarinyar ne ya jawo hankalin maƙwabta, inda suka yi gaggawar zuwa suka ceceta tare da sanar da ‘yansanda.
- Gwamnan Bauchi Ya Gargaɗi Magoya Bayan Wike A PDP
- An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi
Wani mai fafutukar kare haƙƙin yara a yankin, Kabiru Mohammed Abdulkadir, ya bayyana cewa lamarin ya samo asali ne daga iƙirarin ɗiyar matar, wadda ta ce ta ga yarinyar cikin wata ƙungiyar mayu. Ya ƙara da cewa hakan ya haddasa munanan raunuka, inda aka samu al’aura da cinyoyin yarinyar sun ƙone har ma raunukan suka fara ruɓewa, lamarin da ya sa ta kasa yin fitsari da bayan gida yadda ya kamata.
Yarinyar ta na samun kulawa a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), Bauchi, bayan an garzaya da ita domin ceto rayuwarta. Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da cewa an fara bincike kuma za a gurfanar da wacce ake zargi a kotu domin fuskantar hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp