Kaduna ta dau hankalin jama’a a ranar Juma’a yayin da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kai ziyara domin halartar daurin auren Nasirudeen, ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata, Abdul’Aziz Yari Abubakar.
An gudanar da daurin auren ne a masallacin tarihi na Sultan Bello da ke Unguwar Sarki, inda manyan shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya, shugabannin addini da attajirai daga sassa daban-daban na ƙasar suka halarta.
- Sabon Kakin Ƴansanda Ya Ziyarci Cibiyar Ƙungiyar Ƴan Jarida A FCT
- Nijeriya Na Asarar Dala Biliyan 10.5 Sakamakon Rashin Cin Gajiyar Kashin Dabbobi
Shugaba Tinubu, wanda Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya tarba a Filin Jirgin Sama na Kaduna, daga bisani ya samu tarba mai ɗimbin yawa daga magoya bayan jam’iyya da mazauna gari da suka cika tituna suna daga tutoci da rera wakokin goyon baya.
Daga nan ya wuce gidan tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari domin yi wa matar sa Aisha da sauran ‘yan uwa ta’aziyya.

Ya bayyana Buhari a matsayin “shugaba mai kishin ƙasa da sadaukarwa, wanda gudunmawarsa ga haɗin kan Najeriya da ci gabanta ba za a manta da su ba,” inda ya tabbatar da ci gaba da goyon bayansa ga iyalan.
Cikin manyan baki da suka halarci taron har da Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi; Gwamna Umar Bago na Jihar Neja; Gwamna Dikko Radda na Katsina; Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na Kwara da Ministan Tsaro, Bello Matawalle.
Sauran sun haɗa da tsoffin gwamnoni Sule Lamido na Jigawa; Aliyu Wamakko na Sakkwato; Abdullahi Adamu Aliero na Kebbi; Ahmad Sani Yarima na Zamfara; Abdulfatai Ahmed na Kwara da Aminu Bello Masari na Jihar Katsina.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp