A yau Lahadi 21 ga wannan wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka da Adam Smith ya jagoranta a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing.
A yayin ganawar, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da Amurka manyan kasashe ne dake da muhimmanci sosai a duniya, kiyaye dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka mai dorewa yadda ya kamata ya dace da moriyar kasashen biyu da begen kasa da kasa. Sin tana son yin kokari tare da kasar Amurka wajen girmama juna, da zama tare cikin lumana, da yin hadin gwiwar samun moriyar juna. Kana kasar Sin tana son kasar Amurka ta yi hadin gwiwa tare da ita don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata, ta hakan za a amfana wa kasashen biyu da ma duk duniya baki daya. (Zainab Zhang)