Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya isa birnin New York na Amurka da yammacin jiya Litinin, don halartar babban taron mahawara na MDD karo na 80. Yayin da yake birnin na New York, Li zai halarci wasu jerin ayyuka da Sin ta tsara, ciki har da taron manyan jami’ai game da shawarar tsarin shugabancin duniya, kana zai gana da babban magatakardar MDD Antonio Guterres da shugabannin kasashe masu ruwa da tsaki.
Yayin tarukan cudanyar mabanbantan sassa, da na bangaren Sin da daidaikun kasashen, Li zai yi karin haske dangane da mahangar kasar Sin game da yanayin da ake ciki a harkokin kasa da kasa a halin yanzu, da manyan batutuwa da ayyukan MDD. Zai kuma fayyace manufofin kasar Sin na gida da na waje, da ma shawarar da ta gabatar dangane da tsarin shugabancin duniya, da sauran kudurori da shawarwarin da kasar ta gabatar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp