Hukumar Binciken Tsaro ta Nijeriya (NSIB), ta ce rashin gyara da kula da hanyoyin jirgin ƙasa ne ya haddasa hatsarin jirgin Abuja zuwa Kaduna da ya auku a ranar 26 ga watan Agusta, 2025.
Binciken farko ya nuna cewa lalacewar kayan aiki da sakacin Hukumar Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC) wajen yin abin da ya dace, shi ne ya haddasa hatsarin.
- An Kama Tsohon Ɗan Wasan Super Eagles, Victor Ezeji, Kan Zargin Aikata Zambar ₦39.8m
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum 4,383, Sun Ceto 1,138 Daga Hannun Mahara Cikin Wata 3
NSIB ta ce har yanzu ana ci gaba da bincike, kuma rahoton ƙarshe ne zai ƙara bayani tare da shawarwarin da ya dace a dauka.
Rahoton ya nuna cewa hatsarin ya faru ne bayan jirgin ya wuce wurin sauya hanya da aka riga aka sani yana da matsala.
Haka kuma, akwai karafab titin jirgi da suka lalace tun wani hatsari da ya faru a bara, amma sai aka yi musu gyaran wucin gadi kawai.
A lokacin hatsarin karfen sauya hanyar ya karye gaba daya, wanda ya haifar da hatsarin.
Hukumar ta kuma gano cewa duk da cewa direbobin jirgin ƙwararru ne, ba a ba su sabon horo ba.
An kuma gano cewa wasu muhimman kayan aiki kamar na’urar CCTV, na’urar sadarwa da agogo sun samu matsala.
NSIB ta shawarci NRC da ta gyara dukkanin kayan da suka lalace, ta sanya sabbin karafan sauya hanya, sannan ta riƙa horar da ma’aikata akai-akai don gujewa irin wannan matsala.
A lokacin hatsarin, mutane 21 ne suka ji rauni daga cikin fasinjoji 618 da ke cikin jirgin, amma babu wanda ya rasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp