Jiya Talata 23 ga wata ne aka kaddamar da bikin nuna hotuna, da shirye-shiryen bidiyo da matasan sassan kasa da kasa suka dauka mai taken “One World: Shared Future”, wato “Duniya Daya: Makomar Bai Daya”, albarkacin murnar cika shekaru 80 da kafa Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sin, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da hukumomin MDD dake nan kasar suka dauki nauyin shiryawa tare.
Mataimakin shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, a yayin taron da jami’an MDD, da jami’an diflomasiyyar kasa da kasa dake kasar Sin, da wakilan hukumomin majalisar dake nan kasar, da wakilan kafafen yada labaran kasa da kasa suka halarta.
A jawabin nasa, Mista Shen Haixiong ya ce, a shekaru 80 da suka wuce, MDD ta bayar da babbar gudummawa da ba za a iya mantawa ba, a fannonin wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaban duniya, gami da taimakawa cudanyar mabambantan wayewar kai. A nata bangare, kasar Sin tana sauke nauyin dake wuyanta a matsayin mambar dindindin a kwamitin sulhun MDD, tana mara wa majalisar baya wajen jagorantar batutuwan kasa da kasa, da kare ra’ayin cudanyar sassan kasa da kasa, tare da shaida wa dukkanin duniya yadda take sauke nauyi a matsayin babbar kasa.
A nata bangare kuwa, a matsayin muhimmiyar abokiyar hadin-gwiwa ta MDD, kafar CMG ta dade tana kula da harkokin majalisar, gami da gabatar da sakonta zuwa ga dukkanin duniya, da ruwaito rahotanni game da tsarin shugabancin duniya, da kafa gada da alaka tsakanin kasar Sin da dukkanin sassan kasa da kasa.
Ya ce a nan gaba kuma, CMG na fatan ci gaba da kokari tare da MDD, da kafafen yada labaran kasa da kasa gami da matasan duniya, don kawar da bambancin ra’ayi da sabani ta hanyar gabatar da hotuna ko shirye-shiryen bidiyo, ta yadda ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya zai kara shiga cikin zukatan jama’a, da amsa shawarar tsarin shugabancin duniya. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp