Gwamnatin tarayya za ta ɗauki mataki kan masu amfani da takardun bogi, ta hanyar umartar dukkan ma’aikatun gwamnati, hukumomi, jami’o’i da sauran cibiyoyi da su fara tabbatar da ingancin takardun karatun ma’aikata daga ranar 6 ga Oktoba, 2025.
Gwamnatin ta ce ta samar da wata manhaja da za a yi amfani da ita wajen tantance ma’ikatan wanda aka sa wa suna ‘National Credential Verification Service (NCVS)’ kuma wanda za a wallafa bayanan kowanne ma’aikaci a cikin shafin domin dubawa.
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Da Gonaki A Kogi, Ta Tsaida Aiyuka A Legas
- Xinjiang A Shekaru 70: Yadda Yankin Ya Habaka Da Aikin Noma
Gwamnatin ta ce daga yanzu ba za a kara ɗaukar kowanne ma’aikaci ba sai ya samu shedar lambar NCVS.
Wannan domar dai an dogara da kundin tsarin aikin gwamnatin Tarayya bisa ga sashe na 10(1) na dokar Ilimi ta (National Minimum Standards and Establishment of Institutions) ta shekarar 1985.
A baya-bayan nan, an gano cewa sama da mutum 22,500 sun yi amfani da takardun bogi daga jami’o’i marasa izini a Benin da Togo daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp