A ranar Talata 23 ga watan nan ne babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya yi bikin nune-nunen hotuna da bidiyo na MDD a hedkwatar MDD dake birnin New York. Kana, shugaban CMG Shen Haixiong ya ba da jawabi ta kafar bidiyo, a yayin gudanarwar bikin mai taken “Kyakkyawar hadin gwiwa da makomar bai daya”.
Cikin jawabinsa, Shen Haixiong ya bayyana cewa, a farkon watan Satumban bana, kasar Sin ta gudanar da gagarumin bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin kin tafarkin murdiya, kana, CMG ya cimma nasarar gabatar da wannan biki ga masu kallo a duk fadin duniya ta harsuna iri 85, tare da dukkanin kafofin watsa labarai, inda adadin mutanen da aka gabatarwa bikin ya kai biliyan 33 da miliyan 940.
- Tinubu Ya Nemi A Bai Wa Nijeriya Kujerar Dindindin A Kwamitin Tsaro Na Majalisar Ɗinkin Duniya
- Majalisar ECOWAS Ta Shirya Fara Amfani Da Fasahar AI Don Inganta Ayyukan Dokoki
Haka zalika kuma, CMG ya kaddamar da bikin mu’amalar al’umma mai taken “Amsa kuwwar zaman lafiya” a hedkwatar MDD dake birnin New York, domin girmama jarumai, tare da maimaita tarihin bil Adama.
Bugu da kari, mahalarta bikin sun bayyana cewa, bikin ya nuna maimaituwar tarihin MDD na shekaru 80 da suka gabata, tare da yin kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, domin karfafa aniyar al’ummomin kasashen duniya ta kare zaman lafiya, da inganta fahimtar juna.
Haka kuma, Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG, ya shirya wani bikin kade-kaden fina-finai masu alaka da zaman lafiya, mai taken “Hadin kai a duniya, Muryar zaman lafiya”, a cibiyar fasaha ta Lincoln da ke birnin New York na kasar Amurka a daren ranar Talata.
Mataimakin sakantaren MDD mai kula da harkokin watsa labarai, Melissa Fleming, ta taya murnar bude bikin ta kafar bidiyo. Haka kuma, shugaban CMG Shen Haixiong, da jakadan Sin a Amurka Xie Feng sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo.
Shen Haixiong ya bayyana cewa, shekaru 80 da suka wuce, bala’o’in yake-yake guda 2 a duniya, sun sa al’ummar duniya yin tunani mai zurfi, kuma MDD ta samu dalilin kafuwa, hakan nan an bude sabon babi na tsarin shugabancin duniya.
A matsayinta na babbar kafar watsa labarai mai sauke nauyi, CMG ta mai da hankali kan ba da labarin ayyukan MDD da kyau, tare da aiwatar da shawarwari 4 na duniya da Shugaba Xi Jinping ya gabatar. Ya ce, “A yau muna amfani da kida don isar da imanin zaman lafiya, muna girmama nasara ta hanyar wakoki, kuma muna hada kan al’umma ta hanyar fasaha. Ta hanyar tattaunawa, muna karfafa fahimtar juna tsakanin al’adu, kuma muna ba da gudummawa a bangaren watsa labarai ga ci gaban tsarin shugabancin duniya tsakanin mabanbantan bangarori.” (Masu Fassara: Maryam Yang, Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp