Wannan tsumi tabbas yana gyara mace sosai da kara ni’ima da kashe kwayoyin cuta wannan hadi ne na musamman wanda idan mace tana amfani da shi za ta kara samun wadatacciyar ni’ima sannan duk yana kashe kwayoyin cutar gaban mace.
Abubuwan bukata:
- Sassaken baure,
- mazarkwaila,
- Zuma,
- Kaninfari,
- Citta,
- Minannas
Yadda ake hadawa
Za ki zuba sassaken bauren cikin tukunya ki zuba ruwa da yawa sai ruwan ya kusa shanye kansa sai ki dora shi a wuta ki bar shi ya dahu sosai sai ki sauke ki cire sassaken bauren sai ki tace ki zuba zuma , mazarkwaila, da kanunfari gami da citta da minannas. Ana son a zuba kanunfari da yawa a mayar da shi a cikin tukunya a dora a wuta ya kara tafasa sannan ki juye ki rika sha kofi biyu safe da yamma.
In sha Allahu idan kika jure shan wannan za ki kasance cikin ni’ima a koda yaushe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp