Mambobin tawagar gwamnatin tsakiya sun ci gaba da ziyartar jami’ai da mazauna yankuna da dama na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta arewa maso yammacin kasar Sin, da kuma hukumar kula da masana’antu da gine-gine ta Xinjiang (XPCC) a jiya Jumma’a.
Shugaban babban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kana shugaban tawagar ta gwamnatin tsakiya Wang Huning, ya jagoranci wakilan tawagar zuwa biranen Tiemenguan da Beitun da ke karkashin kulawar XPCC.
Wang ya ce, hukumar XPCC ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen karfafa zaman lafiya da walwalar jama’a na dogon lokaci a jihar Xinjiang, yana mai yin kira ga hukumar da ta sauke nauyin gudanar da ayyukanta da kudurorinta a sabon zamani, da zurfafa hade ci gabanta da na jihar, da samar da sabbin alfanu wajen kiyaye zaman lafiya da kare kan iyaka. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp