Yawan ribar da manyan kamfanoni na kasar Sin suke samu ta karu da kashi 0.9 cikin 100 a mizanin shekara-shekara a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2025, lamarin da ya farfado da raguwar da aka samu da kashi 1.7 cikin 100 a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a yau Asabar.
Jimillar ribar da kamfanonin da ke samun makudan kudin shiga na kasuwanci a shekara na akalla yuan miliyan 20 (kimanin dalar Amurka miliyan 2.81) ta kai kusan yuan tiriliyan 4.7 a cikin watannin takwas, a cewar hukumar kididdiga ta kasar Sin.
A cikin watan Agusta, ribar da manyan kamfanonin suka samu ta farfado sosai, inda ta karu da kashi 20.4 cikin 100 a kan ta daidai irin wannan lokacin a bara, idan aka kwatanta da raguwar da aka samu da kashi 1.5 cikin 100 a watan Yuli. Kudaden shiga na kasuwancinsu sun karu da kashi 1.9 bisa dari a mizanin shekara-shekara, watau an samu saurin karuwa da kashi daya a kan na watan da ya gabata, kamar dai yadda bayanai suka nuna. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp