Da yammacin yau Asabar ne manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa Real Madrid da takwararta Athletico Madrid suka fafata wasan mako na 7 a gasar Laliga ta bana a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke birnin Madrid.
Normand na Athletico ne ya fara jefa ƙwallo a ragar Madrid kafin Mbappe ya farke a minti na 25, a minti na 36 Arder Guler ya sake jefa ƙwallo a ragar Athletico kafin Sorloth ya farke ƙwallon dab da tafiya hutun rabin lokaci.
- Tawagar Gwamnatin Tsakiya Na Ci Gaba Da Ziyartar Jami’ai Da Mazauna Yankuna Da Dama Na Jihar Xinjiang
- Masana Sun Dora Alhakin Rashin Cika Alkawuran ‘Yan Siyasa Kan Jam’iyyu
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Julian Alvarez ya ci ƙwallaye biyu a bugun tazara da bugun daga kai sai mai tsaron raga kafin Antoine Griezmanm ya jefa ƙwallonnsa ta farko a wannan kakar kuma ta 5 ga Athletico a wasan na yau.
Da wannan sakamakon Athletico ta koma matsayi na 4 a teburin gasar Laliga da maki 12 yayin da Real Madrid ke ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburin da maki 18 a wasanni 7 da ta buga, idan Barcelona ta lashe wasanta da Real Sociedad ranar Lahadi za ta koma matsayi na ɗaya a kan teburin da maki 19.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp