Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga makarantun horar da ‘yan jam’iyya da su taka rawar gani wajen kyankyashe hazikai, tare da gabatar da shawarwari ga JKS.
Xi, wanda shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin wani umarni da ya gabatar ga makarantun koyar da jagoranci na ‘ya’yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)