Kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya ƙulla sabuwar yarjejeniya ta samar da ɗanyen mai da matatar man Dangote, inda za ta ƙara samar da man na tsawon shekaru biyu a wani mataki da ake sa ran zai ƙarfafa shirin gwamnatin tarayya na sayar da ɗanyen mai kan farashin “Naira”.
Yarjejeniyar wacce aka kammala a watan Satumba, kamfanin mai na gwamnati zai samar wa matatar Dangote da danyen mai jirage 5 a watan Satumba da Oktoban 2025, a cewar kakakin NNPC, Andy Odeh.
Da wannan sabuwar yarjejeniyar, jimillar ɗanyen man da ake samarwa matatar man Dangote a yanzu ya kai ganga miliyan 82 tun daga watan Oktoban 2024, in ji NNPC, inda ta bayyana cewa kashi 60 cikin 100 na man, an sayar ne akan farashin Naira.
A shekarar da ta gabata, Nijeriya ta ƙuduri aniyar samar da gangar ɗanyen mai 445,000 a kowace rana ga matatar a cikin kuɗin gida (Naira).
Jami’an gwamnati sun yi nuni da cewa, shirin, idan ya yi nasara, za a iya fadada shi zuwa sauran matatun mai na masu zaman kansu da ke cikin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp