A yammacin jiya ne, aka bude bikin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na shekarar 2022 wato CIFTIS a takaice a nan birnin Beijing na kasar Sin, inda manyan baki 189 daga ciki da wajen kasar ne, suka halarci bikin, kana kasashe da hukumomin kasa da kasa da yawansu ya kai 71 suka halarci bikin ta hanyar kafa shagunansu.
Bikin CIFTIS na wannan karo, ya jawo hankalin kasa da kasa matuka, manyan kamfannoni fiye da 400 dake cikin jerin kamfannoni 500 mafi karfi a duniya, da sauran manyan kamfannonin kasa da kasa ne, za su halarci bikin.
Game da wannan biki, babban wakilin sashen hukumar farfado da cinikayyar kasar Japan dake birnin Beijing Takashima Ryusuke, ya bayyana fatan yin amfani da wannan dandali wajen gabatar da kayayyaki kirar kasar Japan ga jama’ar kasar Sin, tare da kara fahimtar kasuwar cinikayya ta yanar gizo ta kasar Sin. Ya ce, “Bikin CIFTIS ya kara karade fannoni da dama. Baya ga wannan biki, ana kuma gudanar da taron tattaunawa ko taron nuna sabbin kayayyaki da dama.
Mun fi sha’awar harkokin cinikayya ta yanar gizo. Na halarci wasu taruruka dake shafar wannan fanni, da kara fahimtar yanayin bunkasuwar sha’anin ciniki ta yanar gizo na kasar Sin da manufofin kasar a wannan fanni.”
Yanzu haka, cinikayyar hidimomi ta kasance wani muhimmin bangare na raya hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da kasashen waje, kana ta samar da gudummawa ga raya hadin gwiwa da kuma inganta farfado da cinikayyar hidimomi ta duniya baki daya.
A cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan kudaden cinikayyar hidimomin da aka shigo da su cikin kasar Sin, ya zarce dalar Amurka triliyan 4.
Ban da haka, kasar Sin ta gudanar da bukukuwan CIFTIS a jere, inda ta samar da wannan dandali mai kyau ga kasashen duniya, don karfafa hadin gwiwar cinikayyar hidimomi. (Zainab)