Wata mata mai matsakaicin shekaru ta cinna wa kanta da kanta wuta a cikin gidan Firaministan Nijeriya na farko, marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa, da ke Bauchi, lamarin da ya janyo ajalinta.
Ganau sun ce akwai yiyuwar matar na fama da taɓin hankali wacce ta je gidan a cikin Keke-Napep ɗauke da galan ɗin man fetur.
- Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas
- Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara
An labarto cewa ta je gidan ne da nufin ta ga Hajiya Yelwa Abubakar Balewa, ɗiyar Firaministan wacce kuma ita ce shugaban hukumar kula da marayu da marasa galihu ta jihar Bauchi (BASOVCA).
Ganau sun ƙara da cewa a lokacin da aka shaida wa matar cewa Yelwa ba ta nan, sai ta koma mashigar gidan ta kwarara wa kanta man fetur tare cinna ashana wanda hakan ya janyo wuta ta tashi.
Nan take lamarin ya janyo hankalin mutanen da suke kusa da wurin inda suka yi ƙoƙarin kashe wutar amma lamarin ya ƙazanta.
Daga baya kuma aka kwasheta zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), inda daga bisani ta rasu sakamakon ƙonewar da ta yi.
An kuma ce marigayiyar ɗiyar tsohon wani alkalin kotun Shari’a a Bauchi ce, wacce ta taɓa yin aure har da ‘ya’ya.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil a ranar Alhamis ya tabbatar da faruwar lamarin tare da misalta hakan a matsayin abun takaici.
Ya ce Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya umarci babban Baturen ɗansanda na cajin ofis ɗin ‘A’ Division da ya gudanar da bincike kan lamarin.
A cewar Wakil, binciken farko-farko ya nuna cewa matar na da tarihin matsalar ƙwaƙwalwa, wacce ta samu hakan tun lokacin da ta haihu na ƙarshe.
“An samu nasarar cetota a raye kuma an kaita Uwa je da ita asibitin tana raye ATBUTH, har an ɗaurata kan magani kafin daga bisani rai ya yi halinsa. Muna miƙi ta’aziyyarmu ga iyalanta da addu’ar Allah ya mata raham,” PPRO ya shaida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp