Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta samu nasarar kwato miyagun kwayoyi da kayan maye da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 120 a wasu samame da ta gudanar a fadin jihar.
Kakakin Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce an kuma kama wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a yayin samamen.
- Kasar Sin Ta Nuna Takaici Da Matakin Amurka Na Kin Amincewa Da Daftarin Kudurin Gaza
- Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas
Kiyawa ya ce, jami’an tsaro a kauyen Jalli da ke karamar hukumar Dawakin Tofa sun kwato fakiti 540 da ake zargin kwayar Pregabalin ce, wanda kudinsu ya kai N40,500,000.00.
Rundunar ta kuma bayyana cewa, a ranar 30 ga watan Satumba da misalin karfe 11:15 na safe, wata tawagar rundunar ta kama wasu mutane biyu a filin tirela na Dangauro.

Sanarwar ta kara da cewa, “An samu wadanda ake zargin dauke da buhu bakwai da ake zargin kayan maye ne wanda aka fi sani da ‘Akuskura.’ Ko wanne buhu na dauke da kwalabe 350, adadinsu ya kai kwalabe 2,450, wanda kudinsu ya kai ₦2,450,000.
SP Kiyawa ya kara da cewa, bisa hadin gwiwar hukumomin tsaro, “Rundunar ta mika wadanda aka cafken da kayayyakin su da darajarsu ta kai N120,000,000 ga hukumar NDLEA, ta jihar Kano, domin ci gaba da bincike.”


Hakazalika, jami’an rundunar sun kama wasu fitattun ‘yan fashi da makami da aka bayyana sunayensu da Nura Sani mai shekaru 20 a garin Zango na jihar Bauchi da kuma Ibrahim Lawan mai shekaru 35 daga jihar Katsina.








