Gwamnatin jihar Nasarawa ta raba Naira miliyan 592 a matsayin tallafin karatu ga ɗalibai 16,756 da ke karatu a manyan makarantu daban-daban a faɗin Nijeriya.
Gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ne ya bayyana haka yayin bikin kaddamar da rarraba tallafin a ranar Alhamis a ƙaramar hukumar Akwanga.
- Xi Ya Taya Jami’ar Tianjin Murnar Cika Shekaru 130 Da Kafuwa
- ‘Yansanda Sun Ƙwato Muggan Ƙwayoyi Na Naira Miliyan 120 A Kano
Ya ce, wannan mataki na daga cikin jajircewarsa na zuba jari a makomar ɗalibai tare da sauya tsarin ilimi a jihar.
Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a halin yanzu take ɗaukar nauyin ɗalibai 155 da ke karatu a fannoni daban-daban a ƙasashe daban-daban na duniya.
Ya ƙara bayyana cewa, gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin ɗaliban jinya da kuma wasu a jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar.
“Mun kuma biya kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta shekarar 2025 ga ɗalibai sama da 24,000 na makarantun sakandare na gwamnati, domin rage wa iyayensu nauyi,” in ji Gwamna Sule
Sule ya kuma umarci hukumar da ke kula da tallafin karatu da ta fara aiwatar da tsarin biyan kuɗaɗen ɗalibai na shekarar karatu ta 2025/2026.
A farkon taron, Hajiya Sa’adatu Yahaya, Sakatare mai aiwatarwa ta Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Nasarawa, ta bayyana godiya ga gwamnan bisa wannan kyakkyawan aiki.
Ta bayyana cewa, ɗalibai 25,000 ne suka nemi tallafin karatun ta hanyar manhajar yanar gizo, amma hukumar ta tantance ɗalibai 17,762 bayan yin tsarin tantancewa ta yanar gizo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp