Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana ƙaddamar da motocin bas guda 50 a matsayin cika alƙawari da kuma kawo abubuwan da za su amfani al’umma a nan gaba, wanda ke nuni da jajircewar jihar ta kai wa ƙololuwa.
Gwamnan ya ƙaddamar da sabbin motocin bas guda hamsin masu ɗauke da kujeru goma sha takwas na Kamfanin Sufuri na jihar Zamfara a ranar Alhamis, a Gusau.
- Balaguron Fasinjoji Ta Jirgin Kasa A Kasar Sin Ya Kai Matsayi Mafi Girma A Bikin Ranar Kafuwar PRC
- ‘Yansanda Sun Ƙwato Muggan Ƙwayoyi Na Naira Miliyan 120 A Kano
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa sabbin motocin bas ɗin guda 50 na zamani ne, masu AC da aka ƙera domin jin daɗi da tsaron matafiya.
Sanarwar ta ƙara da cewa, motocin bas ɗin na ɗauke da kujeru masu laushi, an sanya musu bel a kowace kujera, sannan suna jure tafiya a hanyoyi masu gargada, kuma suna ɗauke da na’urorin GPS da zai ba da damar sa ido kan wuraren da suke aiki da kuma yadda suke aiki.
A jawabin sa a wajen ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya jaddada cewa taron ya nuna wani sabon babi a cikin tafiyar Jihar Zamfara, wanda ya bayyana ƙarara irin hazaƙar gwamnatinsa ta barin ɗabi’ar barna da almundahana, inda ta rungumi ɗabi’ar riƙon amana da samar da ci gaba.
Ya ce, “Da yawa suna tambayar dalilin da ya sa aka ɗauki lokaci kafin zuwan waɗannan motocin bas ɗin da kuma jinkirin tsara su yadda ya kamata kafin au fara aiki? A baya, mai yiwuwa gwamnatoci sun yi gaggawar ƙaddamar da su nan take, hankalin su na wajen biki ta datse ribbon ba tare da kafa wani tsarin da ke tabbatar da ɗorewar aikin su ba.
“Amma gwamnatina ta sha bamban. Ba mu yi gaggawa a inda yake buƙatar taka-tsantsan ba. Ba ma rawan jikin da zai iya saka kayan gwamnatin cikin haɗari. Wannan jinkirin da gangan ne.
“Mun zabi da farko mu samar da tsare-tsaren da suka dace na bin diddigi, sa ido, da gudanarwa cikin tsanaki ta yadda abin da ku ke gani a nan zai ɗore kuma ba zai shiga cikin kaddarar motocin da aka saya a shekarun baya ba.
“Tarihin zirga-zirgar jama’a a jihar Zamfara na cike da misalan sakaci. Motocin da aka sayo da kuɗaɗen jama’a sukan ƙare ne ana karkatar da su wajen amfanin wasu ɗaiɗaiku, a ajiye su a harabar wasu gidajen wasu zababbun mutane, a mayar da su ƙarafa marasa amfani ta hanyar tuƙin ganganci, ko kuma a watsar da su domin ba a aiwatar da tsarin kula da su ba.
“Dukiyar talakawa ta zama abin wasa ga wasu ‘yan ƙalilan. Mun yanke shawarar cewa, a ƙarƙashin kulawar mu, ba za a sake yarda da irin wannan rashin ɗa’a ba. Waɗannan motocin bas ɗin za su ci gaba da kasancewa a kan tituna, suna hidima ga mutanen da suka biya kuɗin su da amana, haraji, da kuma kyakkyawan fata.”
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin sa ta wuce sayen injuna, inda ya ce gwamnati ta saka hannun jari a rayuwar mutane.
“A cikin ’yan watannin nan, ma’aikatan Kamfanin Sufuri na Jihar Zamfara, da suka haɗa da na gudanarwa, direbobi, makanikai, jami’an bayar da tikiti, da ma’aikatan gudanarwa, sun gudanar da wani gagarumin shiri na inganta iya aiki, wanda ya mayar da hankali kan fasahar ƙere-ƙere, ɗa’a, hidima, da hanyoyin sarrafa sufuri na zamani.
“Idan harkar sufuri ta lalace, al’umma ta lalace. Ta hanyar ƙarfafa harkokin sufuri, muna ƙarfafa dukkanin vangarorin rayuwa ne a jiharmu.
“Zamfararmu, da ke Arewa maso yammacin Nijeriya, ta haɗe da Sakkwato, Kebbi, Katsina, Kaduna, Abuja, Bauchi, da Gombe, tana a matsayin muhimmiyar cibiyar kasuwanci, ilimi, kiwon lafiya, da zamantakewar jama’a. Sanya motocin bas a nan yana inganta zirga-zirgar gida tare da haɗa ‘yan jihar da sauran al’umma. ‘Yan kasuwa suna samun kasuwa mafi girma, ɗalibai suna halartar cibiyoyin karatu da kyau, iyalai suna ƙara zumunci, kuma ma’aikatan gwamnati suna tafiya wuraren aiki cikin kwanciyar hankali.
“A yayin da muke ƙaddamar da waɗannan motocin bas ɗin, ina kira ga al’ummar Zamfara da su rungume su, su ba su goyon baya, su kare su, kada a barnata dukiyar jama’a ko a yi watsi da su. Ƙazana ƙarfin bas, keta kujerar zama, fasa gilashi, ba asara ba ce ga Gwamnati, amma asara ce a gare mu duka. Mu haɗa gwiwa. Kamar yadda waɗannan motocin bas ɗin su ke na al’umma, haka ma hankalin mu ya zama na al’umma.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp