Matashin É—an wasan gaban Barcelona da Sifaniya, Lamine Yamal zai shafe tsawon mako uku ya na jinyar raunin da ya samu a mararsa.
Yamal na daga cikin ‘yan wasan da tawagar Sifaniya ta kira domin buga wasannin neman gurbin buga gasar Kofin Duniya.
- Xi Da Takwaransa Na Singapore Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 35 Da Kulla Huldar Diflomasiyya
- PENGASSAN Ta Yi Watsi Da Tayin Dangote Na Biyan Ma’aikata Albashin Shekaru 5 Ba Tare Da Yin Aiki Ba
Yamal ya shafe kwanaki yana jinya kafin ya dawo filin wasa a wasan da Barcelona ta doke Real Sociedad da ci 2-1 a gasar Laliga, sannan kuma ya buga wasan da Barcelona ta yi rashin nasara a hannun PSG a gasar Zakarun Turai.
Sakamakon haka Yamal ba zai buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da ƙasar Sifaniya za ta kara da Georgia da Bulgaria a wannan watan in ji Barcelona a ranar Juma’a.
Ana sa ran É—an wasan mai shekaru 18 da haihuwa zai yi jinyar makonni biyu zuwa uku, kocin Spain Luis de la Fuente ya ce tun da farko a ranar Juma’a cewa ba shi da wata matsala da kocin Barcelona Hansi Flick bayan sukar da ya yi kan yadda tawagar Æ™asar ke tafiyar da matashin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp