Yayin da aka fara kayataccen hutun fiye da mako guda a kasar Sin mai lakabin “Golden Week +” daga ranar 1 ga watan Oktoba, babban sakataren kula da sha’anin yawon bude ido na MDD Zurab Pololikashvili, ya bayyana rawar da kasar ke takawa a kasuwar balaguro ta duniya, da kuma babbar fa’idar da yawon shakatawa ke da ita ta fuskar tattalin arziki da al’adu.
Ana sa ran gudanar da balaguro daga kasashen duniya zuwa kasar Sin kimanin miliyan 2 a kullum, da kuma tafiye-tafiyen fasinjoji kusan biliyan 2.36 a duk fadin kasar yayin hutun kwanaki takwas na bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin tsakiyar kaka.
A cikin wata rubutacciyar hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan, Pololikashvili ya yaba da gudummawar da kasar Sin ke bayarwa ga bangaren yawon bude ido na cikin gida da na kasa da kasa. Yana mai cewa, “A wurare da yawa, musamman a Turai da Asiya da tekun Fasifik, masu yawon bude ido na kasar Sin suna tallafa wa kananan sana’o’i da sauran harkokin rayuwa bila’adadin.” Kana ya ce, a sa’i daya kuma, bisa dimbin al’adu da kayayyakin more rayuwa na balaguro masu matsayi na farko a duniya da take da su, kasar Sin ita kanta tana zamowa daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen samun baki masu yawon bude ido.
Da yake karin haske kan shirin samar da yankunan yawon bude ido mafi kyau na MDD, ya ce, an amince da yankuna bakwai na kasar Sin a cikin shirin a shekarar 2024, wanda ya kawo adadin wadanda kasar take da su zuwa 15, adadi mafi yawa da wata kasa take da su a duniya.
Babban jami’in na yawon bude ido na MDD ya kuma ce, kasar Sin kasa ce mai kima da kuma himma a harkokin yawon bude ido na MDD. Kuma tana taimakawa wajen jagorantar bunkasa yawon bude ido a sassan yankin mai fadi, tare da muhimmanta sabbin kirkire-kirkire a fannin.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp