Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zargi shugaban kasa Bola Tinubu da fifita halartar taron siyasa a Jihohin da ke fama da matsalar tsaro a maimakon ziyarar jajanta wa wadanda rashin tsaro ya shafa.
Atiku ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga halartar Tinubu a wajen jana’izar Mama Lydia Yilwatda Goshwe, mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.
Shugaba Tinubu, Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang, da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa a ranar Asabar, sun kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar Yilwatda a Jos, babban birnin jihar Filato.
Mahaifiyar Yilwatda ta rasu a watan Agustan 2025, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, tana da shekaru 83.
Da yake mayar da martani, Atiku ya ce shugaban kasar ya zaɓi ya yi ziyarar jana’izar siyasa maimakon ziyarar jama’ar da taɓarɓarewa tsaro ta shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp