Za a gudanar da taron motoci masu amfani da fasahohin zamani na duniya na shekarar 2025 tun daga ranar 16 zuwa 18 ga wannan wata a birnin Beijing, wanda ma’aikatar kula da harkokin masana’antu da sadarwa ta kasar Sin, da ma’aikatar harkokin sufuri ta kasar, da gwamnatin birnin Beijing suka karbi bakuncin gudanar da shi.
Taken taron a wannan karo shi ne maida hankali kan fasahohin zamani da amfani da su a fannoni daban daban. Taron zai mayar da hankali ga fannonin raya sana’o’i, da fasahohin zamani, da kuma hadin gwiwa. Haka kuma, za a maida hankali ga kirkire-kirkire kan sana’ar motoci kamar su fasahar AI, da sadarwa, da tattara bayanai kan motoci, da mattarar bayanai ta microchip da dai sauransu, kana shugabannin hukumomin gwamnatocin kasashen waje da dama da masana za su gane wa idanunsu sabbin fasahohi a wannan fanni. Har ila yau, a yayin taron, za a gabatar da rahotanni game da kafa tsarin hada motoci da hanyoyi da bayanai, da hada motoci da fasahar AI da sauransu. Haka zalika, za a gwada sabbin fasahohi, da kayayyaki, da tsare-tsare, da yanayin raya wannan sana’a baki daya.
Direktan cibiyar raya sana’ar samar da na’urori ta ma’aikatar harkokin masana’antu da sadarwa ta kasar Sin Qu Guochun ya bayyana cewa, Sin tana fatan yin hadin gwiwa da kasa da kasa don tinkarar kalubale da more damar samun ci gaba tare, yana cewa ta hakan motoci masu amfani da fasahohin zamani za su zama wani bangaren yin kirkire-kirkire a duniya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp