Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, , ya amince da a biya kudi naira biliyan ₦2.321 domin biyan hakkokin fansho, kudin sallama da kuma tallafin mutuwa ga tsofaffin ma’aikata da iyalan ma’aikatan da suka rasu a fadin jihar.
Raban kudin wanda yake karkashin tsarin fansho na hadin gwiwa (CPS) da kuma biyan kudin barin aiki dana mutuwa karkashin tsohon tsarin biyan kudin inda , gwamnatin Kaduna ta riga ta biya jimillar naira ₦6.678bn a shekarar 2025, da kuma jimillar ₦13.5bn cikin shekaru biyu na wannan gwamnatin mai ci.
- Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara
- Nijeriya Ta Zamo Ƙasa Mafi Ƙarancin Tsammanin Tsawon Rayuwa A Duniya
A wata sanarwar manema labarai wanda Kwamishinan Ma’aikatar yada labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya rabawa manema labarai yace kula da jin daɗin tsofaffin ma’aikata na daga cikin muhimman abubuwan da gwamnati ke bai wa muhimmanci, tare da tabbatar da biyan hakkokin su a kai a kai domin rage musu radadin rayuwa.
Maiyaki yace Gwamna Uba Sani ya sha jaddada cewa, tabbatar da mutunci da jin daɗin tsofaffin ma’aikata ba kawai nauyin doka ba ne, har ila yau, nauyin ɗabi’a ne da gwamnati ke ɗauka da muhimmanci.
A cewar Sakataren Zartarwa na Hukumar Fansho ta Jihar Kaduna, Ibrahim Balarabe, yace sabon rukuni na biyan kudi zai amfanar da tsofaffin ma’aikata 661 da iyalan waɗanda suka rasu a matakan Gwamnatin Jiha da ta Kananan Hukumomi naira biliyan 1.736 za a biya ga tsofaffin ma’aikata 511 karkashin tsarin ( CPS) sannan kuma naira miliyan 585 za a biya ga tsofaffin ma’aikata 315 da iyalan mamata karkashin tsarin (DBS).
Hukumar ta bayyana cewa, ga waɗanda ke karkashin fanshon hadin gwiwa na (CPS), hakkokin su za a tura kai tsaye cikin asusun fansho (Retirement Savings Accounts – RSAs) ɗin su, yayin da waɗanda ke karkashin tsarin (DBS) za a gayyace su nan gaba don yin tantancewa kafin a biya su.
A ƙarshe, sanarwar ta bayyana cewa wannan amincewa ta sake tabbatar da jajircewar gwamnatin jihar wajen kare rayuwar tsofaffin ma’aikata, tabbatar da hakkokinsu, da kuma ƙarfafa amincewar ma’aikatan Kaduna da gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp