A yayin taron babbar majalisar kungiyar ciniki ta duniya (WTO), wanda ya gudana a birnin Geneva na kasar Switzerland a ranekun 6 da 7 ga watan nan, bangaren Sin ya yi kira ga mambobin kungiyar da su yi kokarin tinkarar yanayin tangal-tangal a fannin cinikayya da ake fuskantar a duniya, da kare tsarin ciniki da ya shafi sassa daban daban cikin hadin gwiwa.
Wakiliyar kasar Sin a kungiyar ta WTO Li Yongjie, ta ce manufar cinikayya ta kasar Amurka, tana haifar da matsaloli ga tsare-tsaren samar da kayayyaki da kasuwanni na duniya, wanda hakan ya zama babban dalilin da ya haddasa yanayin tangal-tangal a duniya. Ban da haka, kasar Amurka ta yi amfani da matakin karbar karin harajin fito, wajen talastawa wasu kasashe daddale yarjejeniya da ita, matakin da ya lahanta hakkin sauran kasashe. Ta ce kasar Sin tana sanya ido kan matakin Amurka, la’akari da yadda take yunkurin dora karfin kasa a kan ka’idojin duniya.
Sa’an nan, a madadin gwamnatin kasar Sin, Li Yongjie ta gabatar da shawarwari 3, wato na farko, akwai bukatar kara sanya ido kan matakan da ake dauka a duniya a fannin cinikayya. Na biyu kuma, daukacin mambobin kungiyar WTO su jaddada matsayinsu na daukaka tsarin ciniki da ya shafi sassa daban daban, da aka kafa bisa tushen ka’idojin kasa da kasa. Kana shawara ta uku ita ce, a dauki takamaiman matakai don tabbatar da cimma burin da aka sanya gaba ta fuskar raya harkokin kungiyar ta WTO.
A dai taron na kungiyar WTO na wannan karo, kasar Sin ta gabatar da wata takarda, mai bayyana matsayinta game da goyon bayan kasashe masu tasowa, a fannin kare hakkinsu bisa tsarin kungiyar WTO, wadda ta samu yabo daga dimbin mambobin kungiyar. (Bello Wang)