Yau Laraba, jirgin kasa dake sufurin hajoji tsakanin Sin da Turai mai lamba 1293, dauke da kayayyakin motoci, da na amfanin yau da kullum da sauransu, ya tashi daga tashar jiragen kasa ta birnin Erenhot dake jihar Mongolia ta gida ta kasar Sin.
Matakin na nuna cewa, yawan zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Sin da Turai kan layin dogo na tsakiya ya zarce 3000 a shekarar nan ta bana, kwanaki 39 kafin cikar wa’adin hakan na bara. Kazalika, ya zuwa yanzu, tashar jiragen kasa dake birnin Erenhot, ta riga ta samu zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Sin da Turai sama da 3000 a cikin shekaru uku a jere.
A halin yanzu, yawan hanyoyin zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Sin da Turai dake tashar jiragen kasa ta Erenhot, ya karu zuwa 74, wadanda suka hada da birane sama da 70 dake kasashen ketare fiye da 10. A gida kuma, sun yi tasiri ga mafi yawan biranen da layukan dogon suka taso. Tun lokacin da aka fara amfani da jirgin kasa na farko a shekarar 2013, kusan jiragen kasa masu sufuri tsakanin Sin da Turai dubu 21 ne suka ratsa ta tashar, lamarin da ya kara fadada yawan kayayyakin da ake jigilarsu, kuma adadin kayayyaki masu daraja, kamar motoci masu amfani da sabbin makamashi, da manyan injuna, da kayayyakin aiki ya karu daga kasa da kaso 10% zuwa sama da kashi 40%, idan aka kwatanta da lokacin baya. (Safiyah Ma)