A yammacin yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, babban kanar Jiang Bin, ya bayyana cewa, tun daga tsakiyar watan Oktoba, tawagar sojojin ruwan kasar Sin ta 48 wadda ta kunshi jirgin ruwa dake dauke da makamai masu linzami masu tarwatsawa jiragen abokan gaba mai suna Tangshan, da jirgin ruwa dake dauke da makamai masu linzami dake kare sauran jirage mai suna Daqing, da kuma jirgin ruwa dake dauke da kayayyakin agaji mai suna Taihu, za ta tashi zuwa zirin tekun Aden da yankin teku dake kusa da Somaliya don karbar aikin sintiri daga tawagar 47 ta sojojin ruwa ta kasar Sin.
Rundunar sojojin ruwan kasar Sin tana gudanar da ayyuka na hakika don tabbatar da manufar al’umma mai makoma bai-daya a hanyar teku, da kiyaye tsaron hanyoyin tekun kasa da kasa, da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Jiang Bin ya kuma bayyana cewa, Sin da Saudiyya za su gudanar da atisayen soja na hadin gwiwa na “Blue Sword-2025” a kasar Saudiyya a tsakiyar watan Oktoba. Wannan shi ne atisayen soja na hadin gwiwa karo na uku tsakanin sojojin ruwan Sin da na Saudiyya, wanda zai kara sa kaimi ga mu’amalar fasaha da dabaru tsakanin sojojin da ke halartar atisayen, da kuma zurfafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa mai amfani tsakanin sojojin kasashen biyu.(Safiyah Ma)