Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya shirya taron manema labarai na yau da kullum.
Dangane da amincewar da gwamnatin Isra’ila ta yi kan yarjejeniyar kawo karshen rikicin Gaza, ya bayyana cewa, kasar Sin na fatan cimma cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita bude wuta na dindindin a zirin Gaza cikin sauri, don magance matsalar jin kai yadda ya kamata, da sassauta rikicin yankin. Kasar Sin tana goyon bayan duk wani kokari na kasa da kasa kan batun Falasdinu dake taimakawa wajen tabbatar da adalci da kuma kiyaye ikon dokokin kasa da kasa. Ya kuma bayyana cewa, kamata ya yi Isra’ila ta daina duk wani aiki dake kara haifar da sabani da kuma tashe-tashen hankula.
Dangane da jawabin da shugaban yankin Taiwan Lai Ching-te ya yi a ranar 10 ga wata, inda ya sake yada kalaman goyon bayan “‘yancin kan Taiwan”, Guo Jiakun ya ce, maganar Lai cike take da karairayi, inda ya sake bayyana halinsa na “mai janyo matsala”, kuma “mai kawo hadari”, kana “mai kunna wutar yaki”.(Safiyah Ma)