Tun bayan da Gwamna Dauda Lawal ya karɓi ragamar mulkin jijar Zamfara a watan Mayun 2023, jihar ta fara fuskantar wani sabon salo na shugabanci wanda ya shafi kusan dukkan fannoni na rayuwa — daga tsaro zuwa tattalin arziki, daga ilimi zuwa lafiya, daga gyaran hanyoyi zuwa sake gina tsarin gwamnati da al’umma, sannan ga zamanannen tsarin harkar sufuri.
A cikin kusan shekaru biyu kacal, Gwamna Lawal ya kafa tarihin da yawancin mazauna jihar ke ganin ya bambanta da abin da suka saba gani a baya, musamman wajen aiwatar da manufofin da suka tabo rayuwar jama’a kai-tsaye.
Tsaro: Babban fagen da Gwamna Dauda Lawal ya fara tinkara da jajircewa
Ba abin mamaki ba ne cewa tsaro shi ne babban ƙalubalen da jihar Zamfara ta daɗe tana fama da shi. Daga Maradun zuwa Shinkafi, daga Anka zuwa Zurmi, matsalar ‘yan bindiga ta yi ƙatutu na tsawon shekaru.
Da yake karɓar mulki, Gwamna Dauda Lawal ya sanar da cewa “ba za a iya gina tattalin arziki ba idan tsoro ya mamaye ƙasa.”
Tun daga farkon watannin mulkinsa, ya kafa Kwamitin Tsaro na Musamman, wanda ke haɗa jami’an soja, ‘yan sanda, NSCDC da ‘yan sa-kai. Gwamnatin ta samar da motocin sintiri sama da 500, da kayan aikin zamani ga jami’an tsaro.
Har ila yau, an kafa Command and Control Centre a Gusau domin sa ido kan al’amuran tsaro ta hanyar amfani da fasahar zamani. Wannan mataki ya rage hare-hare a wasu yankuna, inda al’umma ke sake komawa gonakinsu da kasuwancinsu cikin natsuwa.
Tattalin Arziki da Ci gaban Sana’o’i
A bangaren tattalin arziki, gwamnatin Dauda Lawal ta mayar da hankali kan farfaɗo da ƙananan sana’o’i da bunƙasa harkar kasuwanci.
Ta ƙaddamar da Zamfara Economic Empowerment Programme (ZEEP), wanda ke bai wa matasa da mata tallafin jari da horo kan sana’o’i kamar ɗinki, noma, kiwo, sana’ar waya da ƙera kayayyakin gida.
Haka kuma, gwamnatin ta buɗe Industrial Cluster a Gusau domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu ƙananan masana’antu, tare da samar da tallafi daga Bankin Noma da na Masana’antu.
A cewar kwamishinan tattalin arziki, “Gwamna Lawal na son ganin Zamfara ta daina dogaro da kuɗin rabon asusun tarayya, ta koma jiha mai samar da abin more rayuwa.”
Ilimi: Sabon salo na sake gina makarantun gwamnati
Fannin ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma. A ƙarƙashin wannan gwamnati, an mayar da hankali wajen gyaran makarantu sama da 200, tare da samar da kujeru, littattafai, kayan koyarwa da gyaran gine-gine.
Gwamnati ta kuma dawo da malamai dubu ɗaya (1,000) da aka bar su ba tare da albashi ba a baya, sannan aka ƙaddamar da shirin “Back to School” domin dawo da yara daga kan titi zuwa aji.
Haka kuma, gwamnatin ta sake gyara Zamfara State University Talata-Mafara, inda aka ƙara sabbin sassa na kimiyya da fasaha tare da inganta wuraren kwana da ɗakin karatu.
Lafiya: Asibitoci suna sake farfaɗowa
A bangaren lafiya, gwamnatin ta ƙaddamar da Free Maternal and Child Healthcare Programme, wanda ke bai wa mata da yara ƙarƙashin shekaru biyar kulawa kyauta a asibitoci.
An gyara asibitoci 14 a faɗin jihar, ciki har da babban asibitin Gusau, da aka sake gina dakin haihuwa da dakin tiyata da kayan aiki na zamani.
Gwamnati ta kuma samar da motocin ɗaukar marasa lafiya (ambulance) a kowace ƙaramar hukuma, tare da tura sabbin ma’aikatan jinya, likitoci da masu jinya zuwa yankunan karkara.
Ayyukan Gina Hanyoyi da Tsarin Gine-gine
Gwamnatin Dauda Lawal ta ƙaddamar da aikin gine-ginen manyan hanyoyi kamar Gusau–Damba–Mayana, Zurmi–Bukkuyum, da Kaura Namoda–Birnin Magaji.
Har ila yau, an gyara titunan cikin garin Gusau, inda aka saka fitilun zamani da tsarin ban ruwa don rage ƙura da datti.
A cewar Gwamna Lawal, “titi ba kawai hanyar mota ba ce, ita ce hanyar ci gaban al’umma.”
Gudanar da Gwamnati da Gaskiya
Wani abu da ya bambanta wannan gwamnati da waɗanda suka shuɗe shi ne gaskiya. A karon farko, Zamfara ta kafa tsarin Open Budget Portal, inda kowa zai iya ganin yadda kuɗin gwamnati ke tafiya.
Gwamnatin ta kuma kafa Anti-Corruption and Due Process Bureau, domin tabbatar da cewa kowace kwangila yana bin ƙa’idar gaskiya da nagarta.
Matsayin Jama’a da Hangen Nesa
Yawancin mazauna jihar sun bayyana cewa wannan gwamnatin “ta shigo da sabuwar rayuwa.” A cewar wani ɗan kasuwa a Gusau, “A baya, an manta da mu gaba ɗaya. Amma yanzu muna ganin canji a zahiri.”
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa burinsa shi ne “Zamfara ta zama misalin tsabta, ci gaba da daidaito a Arewa.”
A tsarin da yake ginawa, ya ƙunshi Zamfara 2050 Vision Plan, shiri mai dogon lokaci da ke nufin canja jihar daga karkacewar tsaro da talauci zuwa jihar da ke iya dogaro da kanta.
Kammalawa
A ƙarshe, shekaru biyu bayan hawansa mulki, Dauda Lawal ya kafa tubalin sabon sahu a Zamfara – sahun da ya haɗa da tsaro, ilimi, lafiya, da tattalin arziki.
Ko da yake har yanzu akwai ɗan burbushin ƙalubale na tsaro da tattalin arziki, yawancin ‘yan Zamfara na ganin cewa wannan gwamnatin ta fara canji daga tushe, kuma abin da ke buƙata shi ne ci gaba da ɗorewar gaskiya, aiki tuƙuru da haɗin kai.
Zamfara tana fuskantar sabon zamani. Kuma idan aka kiyaye wannan tafiya, akwai yiwuwar a ce a cikin ɗan lokaci, Dauda Lawal ya kafa sabon tarihin shugabanci a Arewa.
Rahoto na musamman daga Mahdi Musa Muhammad
Ƙaramin Edita, Blueprint Manhaja