Madugun yankin Taiwan na kasar Sin, Lai Qingde (William Lai), ya yi jawabi a kwanakin baya, inda a hannu daya ya nemi jirkita tarihin babban yakin duniya na biyu, da zummar samar da damar balle yankin Taiwan daga kasar Sin. Kana a dayan hannun kuma, ya kururuta batun da ya kira fuskantar barazanar matakan soja daga babban yankin kasar Sin, don neman kara kudin da yankin Taiwan ke kashewa a fannin aikin soja. Sai dai maganarsa ta janyo dimbin suka daga kafofin watsa labaru na yankin Taiwan, inda suka bayyana Lai Qingde a matsayin mai manta tarihin mulkin mallaka da kasar Japan ta yi a yankin Taiwan, wanda kuma ke neman murguda gaskiyar tarihi daga tushe.
Sanin kowa ne, komawar yankin Taiwan kasar Sin wani muhimmin bangare ne na sakamakon babban yakin duniya na biyu, da na tsare-tsaren duniya da aka tanada bayan yakin. Kana dimbin kundayen dokokin kasa da kasa sun tabbatar da ikon mulkin yankin Taiwan na kasar Sin. Sa’an nan kuduri mai lamba 2758 da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya zartas a shekarar 1971 ya bayyana manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, yayin da yankin Taiwan ke zaman wani bangare na kasar Sin. Bisa la’akari da yadda Lai Qingde a cikin jawabinsa ke neman jirkita tarihin babban yakin duniya na biyu, da kuduri mai lamba 2758, za mu san cewa shi ne mai cin amanar gaskiyar tarihi, wanda ke neman haifar da illa ga tsare-tsaren kasa da kasa.
Sai dai mutanen duniya ba za su taba mantawa da tarihin dan Adam ba, balle ma su bari a jirkita shi yadda aka ga dama. Maganar Lai Qingde da aikace-aikacensa, da tsoma baki da wasu kasashe suke yi cikin batun Taiwan, ba za su taba sauya matsayin yankin na wani bangare na kasar Sin ba, kuma ba za su iya hana dinkewar dukkan yankunan kasar Sin waje guda ba a karshe. (Bello Wang)