A Mali, karancin man fetur ne ya kara ta’azzara a ‘yan makonnin nan, musamman a Bamako babban birnin kasar, wanda hakan rahotanni suka ce yana da alaka ne da karuwar hare-haren kungiyar Jnim, mai alaka da al-Kaeda, a yunkurinta na kokarin hana shigar da mai cikin kasar.
Bayanai sun ce, kusan kowacce rana, mayakan na cinnawa motocin dakon mai wuta, domin ko a ranar Litinin sai da suka kona wata tanka a kusa da garin Sikasso.
- Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina
- Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ASUU Kan Yajin Aiki, Ta Ce “Babu Aiki, Babu Albashi”
A Kayes, Ségou, Mopti, da Gao, ‘yan Mali sun shafe makonni suna kokawa don cika tankunan ababen hawansu., matsalar da hukumomi suka ce ba a taba ganin irinta ba, musamman a babban birnin kasar da ake ganin ne nan ne abin ya fi kamari.
Gidajen mai da dam aka rufe, yayin da wadanda suka kasance da dan sauran mai kuma, layuka ne marasa iyaka suka makare su, lamarin da ta kai har kwana mutane ke yi a gidajen man.
A kan titunan babban birnin kasar, bayanai sun ce ba kasafai ake ganin motoci suna kai komo ba, ko kuma mutane na tura babura, bisa alama dai mutane sun ajiye ababen hawansu a gida.
Sai dai duk da wannan karancin man da ake fama da shi, farashinsa ya ci gaba da kasancewa a yanda yake, domin kuwa farashin lita na mai CFA 775 yayin da dizal yake akan CFA 725.