Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta fitar da alkaluman dake nuna cewa, cikin watanni tara na farkon shekarar nan ta 2025, hada-hadar cinikayyar shige da fice ta hajojin kasar Sin, ta karu da kaso hudu bisa dari a mizanin shekara-shekara, inda darajarta ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 33.61 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 4.73.
Hukumar ta ce ci gaban hada-hadar ya karu ne daga kaso 3.5 bisa dari da aka samu a watanni takwas na farkon shekarar ta bana. (Mai fassara: Saminu Alhassan)